Innalillahi Ya Kashe Mahaifiyarsa Mai Tsohon Ciki Tare Da Kanwarta A Jahar Kano

Qalu Innaillahii Da Dumi Matashin da ya kashe matar babansa A Jihar Kanoa Anguwar rijiyar zaki Alhamdulillah Yanzunnan ya shiga hannun Jami’an Tsaro Yana Kokarin Guduwa Yabar Gari
Rahotanni Sun Tabbatar Da yammacin yau a headquarter yan sanda dake bompait ayi holen wani yaro Matashi dan shekara 20 me suna gaddafi wanda ake zargi da kashe matar baban sa me tsohon ciki da kanwarta jiya a unguwar rijiyar zaki dake birnin kano wannan Al’amari yayi Matukar Daga Hankalin Mutane
Makashin Matashi Gaddafi yace yayi amfani da screwdriver ne wajen Halaka matar baban nasa me suna Rabi’atu me shekaru 24 inda tadinga caccaka mata a wuya da goshi har seda ta mutu gata dauke Da Tsohon Ciki
Gaddafi Ya Kara Da Cewa sannan ya dauko zanin atamfa ya shaqe kanwarta itama har seda tadena numfashi Mutun biyun ta yadda ya Halakasu kenan
Rahotanni Sun tabbatar an sami nasarar kama Gaddafi awani kango yana shirin barin kano mintuna kadan da kashe rabi’a matar babansa da kanwarta nawwara me shekara 8 Allah ya gafartamasu
Al’umma sunshiga yanayin dimuwa da damuwa sakamakon rashin imanin da wannan matashi ya aikata yanzu hakadai yana hannu Jami’an Tsaro Allah yakara shiryamu wanan lamari bema kowa dadiba kuma kowa so yake a gaggauta hukunta Gaddafi dadai da abunda ya aikata
Alhamdulillah Anan zamu dakata da wannan Rahoto A Wannan Lokaci Kucigaba da bibiyar wannan shafi Namu Domin Samun Ingannatattun Rahotanni a kowace rana